ISBN: | 9789789053056 |
---|---|
Imprint: | One-Volume Commentaries |
Format: | Hardback |
Publication Date: | 30/04/2019 |
Pages: | 1852 |
Language: | Hausa |
Sharhin Littafi Mai Tsarki Don Afirka
Publisher: ACTS Nigeria
Sharhin Littafi Mai Tsarki don Afirka muhimmin aikin wallafa ne wanda ya bambanta da saura – bugun farko na sharhi a kan Littafi Mai Tsarki wanda ’yan Tauhidin Afirka suka yi a Afirka domin biyan bukatun fastocin Afirka, ɗalibai, da shugabanni masu tasowa. Ta wurin fassarawa da kuma danganta Maganar Allah bisa ga al’adun Afirka da abubuwan da ake fuskanta a yau, sharhin ya tanada cikakkun bayanai domin fahimtar Maganar Allah waɗanda muhimmancinsu bai tsaya ga Afirka kaɗai ba.
Sharhin Littafi Mai Tsarki don Afirka na da sashe-sashe na fassarori masu dacewa da Africa, waɗanda za a iya karantawa a sauƙaƙe, farashi mai rahusa, tare da kasancewa jagoran Littafi Mai Tsarki gaba ɗaya mai matuƙar anfani. Masu karatu a ko’ina cikin duniya za su amfana tare da yin godiya a kan sababbin bayanai na fahimta da sharhin ya bayar, da salon sharhin na kai tsaye wanda yake kama zuciya da tunani.
Endorsements
Wannan littafin ya sami karabura da yabo daga mutane masu yawa, kuma kayan aiki ne mai matukar amfani ga masu aikin koyarwa da wa'azi a Afrika. Muna gode wa wadanda suka ba da lokaci, karfi, da kuma, himma domin fassara dukkan littadin zuwa harshen Huasa: wannan babban aiki ne kwarai.
Most Rev. Dr. B. A. Kwashi
Bishop na Jos (Anglican Church)
Fassarar wannan littafin zuwa harshen Hausa muhimmin aiki ne, kuma ya kawo ci gaba ga aikin bisharar Ubangiji musamman a fannin shirin wa'azi koyarwa da fassarar kalmonin Littafi Mai Tsarki. Babbar kyauta! Godiya ga Allah!
Rev. Dr. Caleb S. Ahima
Shugaban TEKAN
Ina matukar farin cikin ganin wannan juyi na Africa Bible Commentary a harshen Hausa. Wannan zai zama da taimako ga pastoci masu amfani da harshen Hausa. Zai zama babban kayan aiki ga dukan pastocin da ke son bayyana Maganar Allah cikin duniyarmu ta yau. Saboda haka ina jaddada muhimmancinsa ga pastoci da masu wa'azin Kalmar Allah.
Rev Yunusa S. Nmadu Jnr
General Secretary, ECWA
Ina matukar karfafa kowanne ma'aikacin bishara mai kishin isar da sakon bishara yadda ya kamata, da ya sami juyin Hausa na Africa Bible Commentary. Wannan littafin zai zama kamar abin wasa kayan aiki wadanda ma'aikaci mai himma zai mora cikin aikinsa a gonar Ubangiji.
Most Rev. Musa Panti Filibus PhD
Archbishop, Ikkisiyar Lutheran na Nigeria da Duniya
(LCCN)
Fassar Hausa na littafin Africa Bible Commentary wanda kuke rike da shi a hannuku kayan aiki ne, kuma mataimaki ne wanda ya zo a lokacin bukata, yana bayyana ma'anar Littafin Mai Tsraki ga masu gin harshen Hausa ta hanya mafi saukin fahimta garesu. Kayan aiki ne wanda ya zama wajibi ga kowane fasto da mai bishara masu morar harshen Hausa.
Rt Rev Dr Jwan Zhumbus
Anglican Diocese of Bukuru